A yau hukumar zaben Najeriya ta INEC reshen jihar Imo suka bada sanarwa cewa Rochas Okorocha na jam’iyyar APC ne ya lashe zaben jihar inda ya sami nasara a kananan hukumomin jihar guda 20.
Shi kuma abokin karawarsa Mista Emeka ya sami nasara a kananan hukumomi 6 daga cikin jimillar kananan hukumomin Imo guda 26. Okorocha ya sami yawan kuri’u guda 419,669 a yayin da shi kuma abokin takararsa Emeka na jam’iyyar PDP ya sami kuri’u guda 33,0705.
Tuni shi Emeka din na jam’iyyar PDP a Imo ya amince da sakamakon zaben. To a jihar Abia kuma, wakilin Muryar Amurka Lamido Abubakar Sokoto yace, an bayyana Ikeze na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri’u guda 264,713.
Sai dai sabanin Emeka na jam’iyyar PDP a Imo, shi Alex na jam’iyyar APGA dake Abia wanda ya sami kuri’un guda 180,882, bai amince da sakamakon zaben ba. GAba daya dai garuruwan Imo da Abia suna nan suna ta aiwatar da bukukuwan murna ba tare da tashin hankali ba.
Your browser doesn’t support HTML5