Hukukomi sun ce wasu mutane kuma akalla 20 sun samu raunuka, kuma adadin wadanda abin ya rutsa da su na iya karuwa.
Kungiyar nan ta likitoci masu agajin kasa da kasa, da ake kira Doctors Without Borders a Turance ne ke tafi da asibitin.
A wani al'amarin kuma na dabam, kungiyar Likitocin ta ce wani harin jirgin sama da aka kai ranar Asabar ya rutsa da wata makaranta a lardin Saada da ke makwabtaka da su, ya hallaka mutane 10 tare da raunata wasu kuma 28. Kungiyar Likitocin ta ce wadanda abin ya rutsa da su 'yan shekaru tsakanin 8 da 15 ne.
Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya yi tir da harin na ranar Asabar.
Mai magana da yawun kungiyar gamayyar ya ce an auna harin ne kan sansanin horas da mayakan Houthi.
Gamayyar da Saudiyyar ke jagoranta ta fara kai hare-haren jiragen saman ne a watan Maris na 2015 don kare gwamnatin Shugaban Yemen Abdu Rabu Mansour Hadi, wanda 'yan tawayen Houthi din su ka kori gwamnatinsa daga Sanaa, babban birnin kasar.