Da ya ke jawabi kan manufofin harkokin waje a jahar Ohio ta yankin tsakiya yammacin Amurka mai matukar tasiri a siyasance, Trump ya ce ya kamata Amurka ta shiga kawance da kowace iriyar kasa, kuma ko da a baya sun saba da juna, muddun ta na da niyyar ganin bayan tsattsauran ra'ayin addini.
"Ba za mu bar irirn wannan danyan aikin ya cigaba ba," a cewar Trump.
Ya ce bullowar ISIS na da nasaba ta kai tsaye da irin salon manufofin harkokin wajen da Shugaba Barack Obama da Sakatariyar Harkokin Wajensa a wa'adi na farko, Hillary Clinton, 'yar takarar Shugabancin Amurka karkashin jam'iyyar Democrat, wadda ke kalubalantar Trump a zaben da za a yi ranar 8 ga watan Nuwamba.
Tump ya ce muddun aka zabe shi zai kira babban taro na kasa da kasa na Shugabannin kasashe don bullo da wata sabuwar hanya ta murkushewa da kuma kawar da ta'addanci.
Wannan shirin Trump na auna ISIS a Gabas Ta Tsakiya, na zuwa ne 'yan kwanaki bayan da ya zargi Obama da Clinton da kirkiro ISIS ba tare da wata hujja ba. Wannan zargi ya janyo wani zagaye na caccakar aniyar Trump ta zama Shugaban Amurka, duk da haka sai da Trump ya sake yin wannan zargi a rata ta biye kafin ya ce shagube ya ke yi.