Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa tana zargin gwamnan jihar Umaru Tanko Al-Makura da karya dokoki sabili da haka tana yunkurin tsigeshi.
Ban da zargin karya dokoki majalisar ta kuma zargi gwamnan da yin almundahana da kudaden talakawa. Dan majalisar dokokin jihar Muhammed Baba Ibako ya bayyana kadan daga zarge-zarge 16 da suke yiwa gwamnan.
Gwamnan yana kashe kudi ba akan kai'da ba. Yana sa kanshi yin abun da ya ga dama. Wai yayi anfani da wasu yara, wasu surukansa ya cire kudi har nera miliyan 800. Ya kashe kudin SURE-P ba akan ka'ida ba. Misali ya fitar da nera miliyan 500 ba da wani dalili ba kana ya dawo yana cewa a yi hakuri. Akwai wasu ma'aikata da ba'a sa lissafinsu a kasafin kudi ba amma ya cigaba da biyansu.
Bugu da kari gwamnan ya kori mutane sama da 7,000 daga aiki amma ya kwashi wasu yara domin karan kansa. Majalisa ta umurceshi ya dawo dasu amma ya ki.
Kwamishanan yada labarai na jihar Muhammed Hamza Elayo yace har lokacin da yake magana da wakiliyar Muryar Amurka basu sami wata wasika daga majalisar dokokin ba. Yace basu san abun da suka tattauna a majalisa ba. Basu san abun da suke nema ba har da ma zasu iya mayar da martani. Su dai gwamna yana cika alkawarin da ya yiwa jama'ar Nasarawa da ta zabeshi.
Ga rahoton Zainab Babaji.
Your browser doesn’t support HTML5