A bayanin da tsaohon gwamnan jihar Kaduna ya yi, Janar Jafaru Isah mai ritaya yace, "demokradiyya harka ce ta kyautata wa yan kasa don cigaba a harkar rayuwar al’umar; domin a sami kwanciyar hankali, harkar tsaro, harkar tattalin arziki, kiwon lafiya da abubuwa da yawa da suka shafi raywar al’ummma, amma hakan sai ya zamo da wahala, sai ya kasance shi dan kasa da kansa shi ne ya rungumi hakkin yin wadan nan abubuwa da gaskiya missali, in aka zo wajen zabe ya zabi mutin da yake yi wa kyakyawan zato ba don abin goron da ya bashi ba.”
Akan batun goron da yan siyasa ke badawa don a zabe su kuma ya ce, a halin da ake ciki yanzu idan katsaya wani ya baka abinda zaka ci, lallai kana cikin matatsala. Najeriya kasa ce mai tarin albarku, amma sai ya kasance yan kasar basa moriyar albarkun, idan ka bari wani ya gutsuro daga dukiya da bata shi ba ya baka, hakan ya nuna akwai abinda yake boye wa. Domin ko in har yana da gaskiya goro ba zai sai mai kuri’u ba sai dai halin sa. Duk wanda ya yi haka ya san bai kyautata wa kansa ba.
Ya kara da cewa "kowa ya sai rariya ya san zata yi zuba da yake bayani akan masu karbar goro don a tunanin su wannan ne kadai ribar da zu iya samu daga yan siyaysa. Duk wanda bai zabi mutumni kwarai baya san cewa ba zai waiwaye shi ba don tamkar chiniki suka yi."
Bayan haka Ya kara da cewa abinda ya kamata shine mutane su gaya ma kansu gaskiya, don an ce jiki magayi.