Bayan an rantsar da karin mata uku a matsayin kwamishanoni a jihar Gombe wanda hakan yasa yanzu jihar tana da kwamishanoni biyar ke nan, sai kungiyar 'yan jarida ta mata (NOWOJ) tace zata yi duk abun da zata iya yi domin mata su cimmma burinsu na samu kashi 35 cikin dari a mukaman gamnati kama daga jhohi zuwa gwamnatin tarayya.
Shugabar kungiyar Mrs. Comfort Mukwallo a jihar Gombe tace saura dan kadan su cimma burinsu. Tace yanzu a jihar Gome mata kwamishanoni sun zama su biyar kana kuma akwai mataimaka kusan dubu daya. Abu na gaba da suke so shi ne duk matan da suka fito neman zabe a goya masu baya. Mata suna son su samu wakilci a kowanematakin gwamnat.
A kungiyance zasu taimaka su fadakar da kawunan mutane musamman mata domin su tashi su nemi mukami. Kada su bari wani mukami ya basu tsoro. Babu mukamin da ba zasu iya rikewa ba.
Mata 'yan siyasa irin su Hajiya Fatima Dudu Biga sun godewa gwamnan jihar Gombe Ibrahim Hassan Dankwambo domin karin mata a majalisar zartrwarsa da yayi. A jihar wai matan sun cimma kashi 35 da ake bukata a kasar gaba daya.
Wannan yunkurin na mata na zuwa ne daidai lokacin da jam'iyyar PDP ta samu sabon shugaba a jihar. Baba Sha'aibu Sabulu shugaban PDP yace idan mata sun fito tsayawa takara basa karbar kudi a hannunsu. Ya kira mata su fito su tsaya takara domin suna goyon bayansu.
Ga rahoton Sa'adatu Fawu.