Tun bayan da aka kammala baban taron kasa na jam'iyyar APC inda 'ya'yanta suka zabi shugabanninsu aka soma raderadin cewa tsohon gwamnan na shirin ficewa daga jam'iyyar zuwa ta PDP.
Masu kula da harkokin siyasa suna ganin ficewar tsohon gwamnan ba zai rasa nasaba ba da irin sainsa dake tsakanin tsohon gwamnan da gwamnan jihar na yanzu Ibrahim Kashim Shettima kodayake can baya sun shaidawa manema labarai sun dinke duk wata baraka dake tsakaninsu.
Jiya Litini da rana tsohon gwamnan Sanata Ali Modu Sheriff ya sauka filin jirgin saman Maiduguri wanda tun cikin watan jiya aka rufeshi sabili da dalilan tsaro. Sanatan ya samu rakiyar wasu 'yan majalisar wakilai su uku cikin goma da ake dasu a jihar da wasu manyan masu baiwa gwamnan Bornon shawara da kuma wasu 'yan siyasa da dama.
Sanata Modu Sheriff ya sauka a garin Maiduguri a daidai lokacin da gwamnan jihar Ibrahim Kashim Shettima ya kama hanya zuwa Kano inda zai shiga jirgi zuwa kasar Saudiya domin yin umura.
Wakilin Muryar Amurka ya tambayi Sanata Sheriff dalilin zuwansa Maiduguri a daidai wannan lokacin. Yace ya zo ne ya bayyanawa mutane cewa jam'iyyar da suka kawowa jama'a, wato gamayyar jam'iyyun da suka hade suka zama APC ba zata iya zama jam'iyya ba. Yace abun da babu gaskiya ciki ba zai yiwa mutane anfani ba. Bai ga alamar APC zata iya biyan bukatar jama'a ba. Yace babu yadda za'a ce duk jam'iyyun Najeriya suna karkashin mutum daya.
Dangane da lokacin da zai koma jam'iyyar PDP Sanata Ali Modu Sheriff yace suna magana da gwamnatin tarayya da shugabannin jam'iyyar amma sauran abubuwan sai bayan azumi. Lokacin ne yace zai gayawa mutane cewa abun da suka fada masu can farko akwai kuskure ciki sabo da haka su koma PDP su gyarata.
Yace batun wai sun kafa jam'iyyar APC da gwamnan jihar na yanzu bai taso ba domin Allah ne mai komi. Yace ai gwamnan yanzu kwamishana ne a karkashinsa na tsawon shekara biyar. Yace bisa ga taimakon Allah shi ya wuce gaba yace a zabeshi ya zama gwamna kuma Allah ya bada ikon a yi hakan. Maganar cewa tare suka kafa jam'iyya bata taso ba. Yace lokacin da shi ya soma siyasa gwamnan yanzu ko makaranta bai gama ba. Yace abun da al'ummar Borno suke so shi zai yi a kowane lokaci.
Ga rahoton Haruna Dauda Biu.