Razumkov, darektan wani kamfanin bada shawarwari a kan harkokin siyasa, ya fara shiga siyasa ne a matsayin tsohon dan jami’iyar tsohon shugaban kasar mai kawance da Rasha Viktor Yanukocych, wanda zanga zangar Maidan ta kawo karshen mulkin sa ya kuma arce zuwa Rasha a shekarar 2014.
Dan wasan barkwancin da bashi da wata kwarewar siyasa a baya, Zelenskiy ya ba shugaban kasar kashi da rata mai yawa a zagaye na biyu na zaben shugaban kasa a ranar 21 ga watan Afrilu.
Wuni guda bayan an rantsar da shi a ranar 20 ga watan Mayu, ya sanya hannu a kan dokar da ta rusa majalisar dokoki kana ya ajiye ranar 21 ga wata Yuli a gudanar da zaben majalisar.
Yin zabe da wuri zai baiwa Zelenskiy dama samun tasiri a farko farko wa’adinsa na shekaru biyar, ta hanyar samun goyon baya a majalisar kasar mai yawan al’umma miliyan 44, wacce take kara fuskantar matsin lamba daga Rasha, kana tana fama da matsalolin tattalin arziki da cin hanci da rashawa.