Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ra’ayoyi Shugaba Donald Trump Sun Bambamta Da Na Firaiminstan Japan Shinzo Abe


Shugaba Donald Trump Da Firaiminstan Japan, Shinzo Abe
Shugaba Donald Trump Da Firaiminstan Japan, Shinzo Abe

A Lokacin da yake Magana a taron manema labarai bayan tattaunar da suka yi a Tokyo, Trump ya ce shi yadda yake kallon gwaje-gwajen makaman na Korea, dabara da shugaba Kim Jong Un ke nuna ta neman a kula shi.

Shugaban Amurka Donald Trump, da Firaiminstan Japan Shinzo Abe, sun bayyana ra’ayoyi mabanbanta a yau Litinin kan ko gwaje-gwajen makamai masu linzami da Koriya ta Arewa ta yi sun karya ka’idojin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, amma kuma sun ci gaba da hada kansu kan abin da ake so a cimma na kawar da makamai masu linzami a yankin ruwan Koriya.

A Lokacin da yake Magana a taron manema labarai bayan tattaunar da suka yi a Tokyo, Trump ya ce shi yadda yake kallon gwaje-gwajen makaman na Korea, dabara da shugaba Kim Jong Un ke nuna ta neman a kula shi, saboda haka ba ya damuwa da su.

Sai dai Abe ya ce gwaje-gwajen sun take ka’idojin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya.

Ya kuma sake jaddada cewa a tattaunawar da ake yi da Koriya ta Arewa, gwamnatinsa ta fi mayar da hankali ne kan yadda za a saki wasu ‘yan Japan da Korea ta Arewa ta ke rike da su.

Jawaban Trump sun maida hankali ne kan batutuwan tattalin arziki, inda ya bayyana yiwuwar cimma yarjejeniyar cinikayya tare da Japan da China domin rage gibin cinikayyar da ya ce ana kwarar Amurka.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG