Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kai Hari A Wani Masallacin Kabul Yau Jumma'a


Jami'ai a kasar Afghanistan sun ce wani bam ya tashi a wani masallacin Kabul dake cike makil a lokacin da ake sallar Jumma’a, inda ya kashe wani babban malami mai goyon bayan muradan gwamnati, da kuma wasu masu ibada da yawa.

Ma’aikatar harkokin cikin gidan kasar da mazauna babban birnin na Afghanistan, sun bayyana cewa, malamin da aka kashe, wato Mawlavi Samiullah Rayhan, yana cikin jagorantar sallar Jumma’a, bam din ya tashi.

Harin ya jikkata akalla mutane 16. An kuma bada rahoton cewa wasu daga cikinsu na cikin “mawuyacin hali."

Na take dai ba’a sami wanda ya dauki alhakin kai harin ba, wanda jami'an kasar suka ce da alama harin ya auna Rahyan ne. An ce malamin na goyon bayan gwamnatin Afghanistan sosai da kuma jami'an tsaron kasar da ke fafatawa da 'yan kungiyar Taliban.

A wani lamari na daban, wata fashewa a yankin yammacin Pakistan ta yi sanadiyar mutuwar akalla mutane 2 tare da jikkata mutane fiye da sha biyu. ‘Yan sanda sun ce harin na yau Jumma’a a unguwar Pashtoonabad dake Quetta ya lalata wani masallaci wanda mazauna garin suka taru don sallar Jumma’a, da kuma gine-ginen dake kusa.

Quetta shine babban birnin lardin Balochisatan dake fama da tashe-tashen hankula, yankin da ‘yan aware suka dade suna gwagwarmaya a cikin sa, wuri ne kuma da wasu kungiyoyin ‘yan bindiga dabam dabam ke aunawa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG