Amurka ta ce akwai alamun da ke nuna cewar, gwamnatin Bashar al-Assad a Siriya na amfani da makamai masu guba kuma ta gargadi Siriyawa su dakatar da shi.
A jiya Talata ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta ce, ta yi imanin cewar, sojojin Siriya na da hannu a wani harin da ake zargin na iska mai guba ne mai suna Chlorine Gas da aka kai ranar Lahadin da ta gabata, a arewa maso yammacin Siriya.
Mai magana da yawun Amurka ta ce, jami'ai suna ci gaba da tattara bayanai game da harin da ake zargin Syria da kaiwa, amma ta ce "idan gwamnatin Assad ta yi amfani da makamai masu guba, Amurka da abokanta za su dauki mataki cikin sauri da kuma dacewa."
Facebook Forum