Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Firayim Ministar Birtaniya Theresa May Za Ta Yi Murabus


Firayim Ministar Birtaniya, Theresa May ta ce, za ta yi murabus daga mukamin firayim ministar kasar, bayan da ta kasa shawo kan 'yan majalisa dokokin kasar har sau uku akan batun neman goyon bayan yarjejeniyar fidda Britaniya daga tarayyar turai.

"Yanzu na gane cewa, don ci gaban kasa, akwai bukatar wani sabon firayam minista ya jagoranci gwagwarmayar kasar, a cewar May "idon ta cike da hawaye.” A saboda haka, a yau ina sanar da cewa zan yi murabus daga matsayin shugabar jam’iyyar Conservative and Unionist ranar jumma’a 7 ga Yuni."

Mako mai zuwa za a fara shirin zaben sabon shugaban jam'iyyar, wanda zai kuma zama Firayim Minista.

A wata sanarwa da ta yi a wajen gidan ta dake Downing Street, May ta ce, abin takaici ne matuka a gareta saboda bata iya cimma yarjejeniyar ballewa daga Turai ba.

Murabus din da May tayi ya janyo gwagwarmayar, ga wanda zai zama sabon firayim ministan Britaniya yanzu, wanda kuma May ke fatan zai sami nasara inda ta gaza.

Theresa May ta zama shugaba ta 3 a jam’iyyarta ta masu ra’ayin ‘yan mazan jiya da ta fuskanci rarrabuwa kai a jam’iyyar akan batun kasancewar Birtaniya cikin tarayyar turai, ita ma ta bi sahun Margaret Thatcher (saacha) da David Cameron.

Kuma zata ci gaba da zama a matsayin shugabar gwamnati a lokacin da shugaban Amurka Donald Trump zai kai ziyara Britaniyya a wata mai zuwa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG