Yayin da ake murnar ban kwana da cutar Ebola a wasu kasashen ‘yammacin Africa, kwatsam kuma sai ga cutar Zika ta kunno kai.
Wannan yasa yanzu haka masana harkokin kiwon lafiya da hadin kan gwamnatoci daukar darasi daga abinda ya faru lokacin yaki da cutar Ebola domin yakar cutar Zika.
Bincike ya tabbatar da cewa dai cutar ta Zika har ta kashe wasu mutane ko yayin da cutar ebola daga zuwan ta har lokacin da akaga bayan ta ta kashe mutane sama da dubu 11.
Kamar yadda jamiin kiwon lafiya Naomi Tegbeh ke cewa suna ganin mutane suna mutuwa kusan kullun a kasar Liberia kana wasu na fama da zazzabi.
Tace kullun akayi batun cutar ebola sai ta zubar da hawaye idan ta tuna yadda mutane suka wahala sakamakon wannan mummunar cutar.
Dr Tom Freiden na cibiyar yaki da cututtuka yace kasashen nan ukku da cutar ebolatayi Kamari sun samarda hanyar yaki da ita kain da na in wanda zaiyi wahala a sake ganin wannan cutar ta bullo.
Yanzu haka dai wadannan kasashen suna da asibitoci masu kyau kana suna da dakunan bincike masu nagarta, tare da kiwon lafiya mai inganci.Yace sanyin jikin kasashen dake bada gudun mowa su da hukumar lafiya ta duniya shine yasa cutar ta ebola ta samu dama har tayi banner da tayi.
Yace sai dai yanzu hukumar ta lafiya ta duniya wato W H O ta riga ta ayyana cukar zika a matsayin cuta ta duniya dominko itatana fara illa ne ga jarirai, amma kuma sai dai masana kiwon lafiya sunce matakin da ya dace a dauka yakamata ya ace wuce da haka.