Ana Muhawara Kan Ko Shugaban Kasa Zai Iya Yafe Wa Kansa Laifi a Amurka

Shugaban Amurka Mai Barin Gado, Donald Trump.

Sabanin yadda a baya aka yi ta muhawara, kan ko shugaban kasa zai iya yafe wa kansa laifi, yanzu abin ya zama muhimmiyar muhawara tun bayan da magoya bayan Trump su ka fusata tare da afkawa ginin Majalisar Dokokin Amurka.

Zanga-zangar magoya bayan Trump ta sa ya shiga tarihi, na zama shugaban kasar na farko da aka taba tsigewa sau biyu a wannan makon, tare da yin kira da a gudanar da bincike kan rawar da Trump ya taka a zanga-zangar.

Wannan kuma ya saka ayar tambaya kan ko Trump zai iya amfani da karfin mulki na shugaban kasa ya gafarta wa kansa, don gujewa tuhuma a gaba.

Don kuwa yin hakan zai sa ba za a iya bincikarsa ba, ko a shekarar 2018 mai bincike na musamman kan zaben 2016 da alakar kwamitin kamfen din Trump da Rasha, inda Trump ya ce zai iya gafarta wa kansa.

Kamar yadda ake ji, gafarta wa kai ba zai taba zama alkhairi ga Trump ba, don kuwa masu bashi shawara sun yi iya bakin kokarinsu su don ya bar wannan maganar. Suka ce gafarta wa kai, yana nuna cewar mutum ya amsa laifin kenan.

Hakan kuma zai sa sabuwar gwamnatin Biden, ta ce sai ta binciki laifin da ya gafarta wa kansa akan su, a cewar masana.