Ana Kara Samun Kwararar 'Yan Gudun Hijira A Kasashen Afrika

Yayin da ake bukin tunawa da ranar ‘yan gudun hijira ta duniya a yau Alhamis 20 ga watan Yuni. ‘Yan gudun hijirar Mali da Najeriya masu sansani a jamhuriyar Nijar, sun koka akan yadda ake ci gaba da kara fuskantar hare haren ta’addanci a yankunan da suka fito.

Lamarin da suke ganinsa a matsayin wata babbar barazana ga shirin komawar su gida, duk kuwa da irin matakan da hukumomin kasashen Sahel ke ikirarin suna dauka, don kawo karshen wadanan tashe tashen hankulan.

Dubun dubatar mutanen da suka tsere daga yankin arewa maso gabashin Najeriya, sanadiyar hare haren kungiyar Boko Haram ne ke hijira a yankin Diffa, dake kudu masu gabashin jamhuriyar Nijar, sai rikicin rikicin arewacin Mali da ya tilastawa dubban ‘yan kasar tsallakawa zuwa yankunan Tilabery, da Tahoua a Nijar kasar da aka wayi gari mutanen suna kaura daga garuruwansu don gujewa aika aikar.

'Yan ta’adda kafin daga bisani masu satar shanu da mutane a jihohin Zamfara, Sokoto da Katsina su tilastawa bayin Allah, zuwa neman mafaka a jihar Maradi a cewar Alhaji Laouan Magaji shine ministan ayyukan jin kai a Nijar.

Shekaru fiye da 6 kenan da Nijar ta fara samun bakoncin ‘yan gudun hijirar Najeriya, lamarin da a halin yanzu wasu ‘yan gudun hijira irinsu Malam Ibrahim dake sansanin Toumour suka fara kosawa da shi.

Shugaban kungiyar ‘yan gudun hijirar Mali a Nijar Waladogaz Killi da na tuntuba akan shirin komawarsu gida cewa yake lokaci bai yi ba.

Mutane miliyan 68.5 ne suka tserewa matsugunansu a shekarar 2017, a cewar Majalisar Dinkin Duniya, yayin da a bana aka kiyasta ‘yan gudun hijira miliyan 70.8 abun da ke nuna wannan matsalar tana karuwa a kowace shekara.

Your browser doesn’t support HTML5

A jamhuriyar Nijar 'yan gudun hijira daga Najeriya da kuma kasar Mali sun nuna damuwa