A yau Talata ne akayi jana’izar Mohammed Morsi, tsohon shugaban kasar Masar, farar hula na farko da aka taba zaba a kasar, wanda kuma aka tunbuke daga kan mulki, ya rasu jiya bayan yanke jiki da yayi a cikin kotun kasar.
Wani daga cikin lauyoyi masu kare Morsi din, yace iyalin Morsi da dama sun halarci jana’izar a masallacin gidan yarin Tora, da ganan aka bizne shi a wata makabarta dake birnin Nasr.
Dan shi Ahmed, yace hukumomi sun hana ayi jana’iazar shi a makabartar iyalansa, dake mahaifarsa a lardin Sharqia, sai suka sa aka birne shi a wata makarabarta ta sannanun jagabannin kungiyoyin ‘yan kishin Islama.
Jami’an sunce Moris mai shekaru 67, yayi ma kotu bayani akan laifin leken asirin kasa da ake mishi, kamin da ga bisani ya yanke jiki ya fadi. Sun ce Morsi yayi maganar mintoci 5 daga cikin wani keji mai gilashi, daga bisani sai ya fadi kasa.
Facebook Forum