Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Gudun Hijira Na Cigaba Da Fama


A South Sudanese refugee woman sits with her child at a refugee collection center in Palorinya, Uganda, Feb. 16, 2017.
A South Sudanese refugee woman sits with her child at a refugee collection center in Palorinya, Uganda, Feb. 16, 2017.

Yayin da duniya ke ikirarin taimaka ma 'yan gudun hijira, har yanzu matsalolinsu sai karuwa ke yi saboda, kamar yadda masu iya magana ke fadi, idan dambu ya yi yawa ba ya jin mai.

'Yan gudun hijira sun sha gamuwa da matsaloli iri-iri, kama daga masu kaiwa ga rasa rai ko munanan raunuka, fyade, zuwa masu kawo asarar dukiya.

Wata 'yar Sudan mai suna Alawiyya Ahmed, ta gamu da wasu daga cikin munanan matsalolin da yan gudun hijira kan gamu da su.

Alawiyyu ta na da juna biyu a lokacin da ta bar Sudan da fatan isa Turai. Sau uku ake kona gidansu kurmus a yankin Darfur don haka daga bisani mijinta, Ahmed, ya yanke shawarar cewa za su jaraba neman wata makoma a Turai. Yanzu tana zaune a Libya a cikin dubban matafiya da suke jira su dau jirgin ruwa su tsallaka teku. Ga dai fassarar rahoton wakiliyar Muryar Amurka Heather Murdock daga birnin Tripoli.


Alawiyya tana da ciki a lokacin da ta gudu daga kasarta Sudan a bara. An kona gidansu sau uku, bayan haka ne mijinta Ahmed ya kawo shawarar barin kasar domin su je Turai su samu rayuwa mai inganci.

Yanzu tana zaune a wani ginin makaranta da aka mai da shi sansanin tare da wasu mutane daga kasarta ta Sudan da Eritrea da wasu kasashe. Dukkanin su sun tsere ma yaki ne da tsananin talauci ko sauran bala'o'i kuma kuma dukkanninsu sun sake rasa matsugunai a cikin watan Afrilu lokacin da yaki ya barke a Libya.

Hukumar kula da harkokin kaurar jama'a ta kasa da kasa ta ce a cikin wannan shekarar, kusan mutane dubu 40 ne suka yi kokarin tsallaka tekun meditariniya zuwa Turai. Wasu ‘yan dubbai ne kadai su ka samu isa Turai, mutane sama da 550 suka mutu.

Amma ga ita Alaweiah ba ta ganin tsallaka tekun a matsayin tafiya ce mai tattare da hadari.


Ta ce da shigowarsu kasar Libya tare da mijinta da ‘ya’yansu mata biyu, ‘yan bindiga su ka kama su suka daure su, su ka bugi mijinta tare da banka masa wuta sannan su ka sace masu kudi. An yi wa Alaweiah (Alawiyya) fyade akai akai har sai da ta yi bari. Wani sa'in ma har tilasta mijinta ake yi ya kalli yadda ake mata faden.

Bayan da su ka gudu, sai su ka gane cewa Alawiyya ta sake daukar ciki da daya daga cikin wadanda suka mata fyaden.

Alawiyya ta ce mijinta ya so su zubar da cikin amma ta ki, don haka ya tafi ya barta cikin fushi. Ta ce bata sani ba ko an yi garkuwa da shi ko kuma an kashe shi ko kuwa dai ya yi watsi da iyalansa ne kawai ba.


A lokacin da nakuda ta kamata, bata da kudin zuwa asibiti, a don haka ta haifi jinjirin ne a kan titi, inda wasu motoci suke tsaye ta samu kariya.


Bayan watanni shida da haifuwar danta, tana rayuwa ne a cikin Tripoli da wata ‘yar karamar sana’ar share share kuma ta kama gida.

Amma a cikin watan Afrilu, sai gashi yaki ya barke bayan da sojojin gabashin kasar suka danno da zummar kwace babban birnin kasar. Yanzu ana ci gaba da gwabza yaki kuma babu alamun wani bangare na gab da yin galaba.

Nan ne kuma wadannan mutane kamar su Alawiyya suka sake rasa matsugunansu.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG