Kotun kolin Pakistan ta kawo karshen sauraron karar aikata cin hanci da rashawa da ka iya sauke Fara Minista Nawaz Sharif ta kuma haramta masa tsayawa takarar siyasa a kasar.
Alkalai ukun da suka saurari karar basu fadi lokacin da zasu sanar da hukuncin da suka yanke ba.
Da yake jawabin karshe, ‘daya daga cikin alkalan yayi alkawarin cewa zasu duba yiwuwar haramtawa Sharif shiga duk wasu harkokin siyasa a wani bangare na shari’ar.
Sharif dai ya musanta aikata duk wani laifi, matsayin da lauyoyinsa suka yi ta nanatawa a lokacin wannan shari’ar da ta kwashe mako guda ana yinta.
Sai dai kumalauyan dake wakiltar jam’iyyar da ta shigar da ‘kara ta Tehreek-e-Insaf, na da kwarin gwiwar cewa za a samu Fara Ministan da aikata laifi a kuma haramta masa shiga duk wasu harakoki na siyasa.