Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fadar White House Tayi Kwauron Bayani


Georgia/US -- Donald Trump US president and Georgian soldier Eldar Saganelidze, undated
Georgia/US -- Donald Trump US president and Georgian soldier Eldar Saganelidze, undated

Fadar Shugaban Kasar Amurkataki ta bada cikakken bayanin abinda Shugaba Donald Trump Suka tattauna da takwarar sa na kasar Rasha

Fadar shugaban Amirka ta White House taki bada cikakken bayani a kan ganawar da shugaba Donald Trump da shugaban Rasha Vladmir Putin suka yi a wurin wani liyafar cin abincin dare da aka yi a wajen taron kasashe masu karfin tattalin arziki na G20 a farkon wannan wata.

Wannan liyafa ce ta jama’a, a cewar mai magana da yawur fadar White House Sarah Huckabee Sanders a bayanin da ta yi wa manema labarai wadanda suka matsa mata a jiya Laraba a kan wannan ganawa da shugabannin biyu suka yi.

Wani daga cikin kusoshin jami’iyar Democrat a kwamitin tattara bayanan sirrin a majalisar wakilai Adam Schiff yace, ya yi mamakin jin wannan ganawar.
Adam Schiff ya dora a shafinsa na sada zumunta na Twitter cewar wannan ne Trump ke kira bayyana gaskiya.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG