Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Bukaci Sauran Kasashen Duniya Da Su Sauya Tunaninsu Kan Africa


Taron shugabannin Africa a kasar India.
Taron shugabannin Africa a kasar India.

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi kira ga kasashen duniya a wani taron majalisar, yana mai cewar su sauya tunaninsu game da nahiyar Afrika.

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya ce ya kamata kasashen duniya su yi aiki tare da nahiyar Afrika kuma su gane irin abubuwa da Afrika za ta iya yi kana su taimaka wurin hanawa da kuma kawo karshe yake-yake da ke addabar yankin.

Antonio Guterres ya fadawa mahawarar Kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya ya yi a kan inganta zaman lafiya da tsaro a Afrika cewar, kungiyar Tarayyar Afrika ta AU da majalisar suna da manufa na ganin cewa sun magance rikice-rikice kafin su yi kamari da kuma fannin yadda za'a tunkare su bayan sun faru.

Karfafa guiwan Afrika yana da muhimmanci a wurin yin aiki tare na magance kalubalan zaman lafiyar kasa da kasa da tsaro da kuma batun dogaro da kai a nahiyar Afrikan.

Ya kuma lura da irin matsalolin da kungiyoyin 'yan ta’adda da masu tsaurin ra’ayi suka kawo.

Guterres ya yi marhabin da shirin kafa rundunar hadin guiwa da kasashen yankin Sahel guda biyar suka yi domin yaki da ta’addanci, da kuma dakarun hadin guiwa na kasashen tafkin Chadi masu yaki da 'yan Boko Haram

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG