Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Qatar Ta Sauya Dokokinta Na Yaki Da Ta'addanci


Ministan harkokin wajen kasar Qatar Sheikh Mohammed bin Abdulrahman al-Thani
Ministan harkokin wajen kasar Qatar Sheikh Mohammed bin Abdulrahman al-Thani

Qatar ta sauya wasu dokokinta da suka jibinci ayyukan ta'addancin a wani mataki na ganin ta dawo da dangantakar ta da Saudi Arabia da wasu kasashe uku na yankin Gulf da suka maida ita saniyar ware.

Sarkin Qatar Sheik Tamim bin Hamad al-Thani ya fitar da wata sabuwwar dokar da za ta yi wa ayyukan yaki da ta'addanci kwaskwarima a kasar.

Dokar ta hada da ma'anar kalmar ta'addanci da dan ta'adda da mai aikata manyan laifuka da rufe asusu da kuma kalaman samar da kudade domin tallafawa ayyukan ta'adanci.

Wannan wani sabon yunkuri ne da kasar ta Qatar ta yi na kaucewa zargin da ake yi mata na cewa tana marawa ayyukan ta'adanci baya.

Kasashe hudu da suka hada da Saudi Arabiya da Hadaddiyar Daular Larabawa da Masar da Bahrain ne ke zargin kasar ta Qatar, zargin da ta sha musantawa.

A makon da ya gabata Qatar ta kulla yarjejeniya da kasar Amurka domin su hada kai wajen yakin da ayyukan ta'addanci, Sai dai kawo yanzu ba cikakken bayanin wannan tsarin da aka cimma.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG