Zaben shugaban kasar da za a yi gobe Alhamis a Kenya shine karo na biyu a cikin wannan shekarar bayan da kotun kolin kasar ta yi watsi da sakamakon zaben da aka yi a baya, ta ce yana cike da magudi.
WASHINGTON DC —
Kotun kolin kasar Kenya ta gaza sauraron karar da aka shigar akan neman ta dage zaben shugabancin kasar da ake shirin yi, hakan ya share hanyar a gudanar da zaben gobe Alhamis idan Allah Ya kaimu.
Babban alkalin kasar David Maraga, ya fadi cewa cikin alkalai bakwai da ake da su, biyu ne kawai suka je kotu, hakan ya gaza adadin alkalai biyar da ake bukata don yanke hukunci.
Wani alkali kuma ya ce nade-naden jami’an hukumar zaben da aka yi don zaben na gobe alhamis, ba bisa ka’ida aka yi su ba.
Sai dai hukumar zaben Kenya ta ce nade-naden na bisa ka’ida kuma jami’an zasu gudanar da harkokin zaben shugaban kasa da za a yi gobe.