Kwamandan sojojin Sudan ta Kudu wanda karkashin kulawarsa ne aka zargi sojoji da laifin kashe wani ‘dan jarida da kuma yiwa a kalla mata ma’aikatan agaji hudu na kasa da kasa fyade a shekarar da ta gabata, ya mutu a cikin gidan wakafinda ake tsare da shi.
Da farko dai an samu gawar Lautanal Luka Akechak, mace a inda ake tsare da shi tun sama da mako guda da ya gabata, amma sai ranar Juma’a aka fitar da rahotan mutuwar.
Kakakin rundunar sojan kasar, Col. Santo Dominic yace ba wata alama dake nuna cewa akwai wata tabargaza wajen kisan nashi.
“Luka Akechak dai ya mutu. Kuma mutuwar ajali ce.” A cewar Domic lokacin da yake magana da Muryar Amurka.
hine babban wanda ake zargi a ta’asar da sojojin Sudan ta Kudu suka aikata, wanda hakan yake nuna yadda yake da matukar wahala wajen gabatar da wadanda ake zargi take hakkin bil Adama ga shari’a a kasar, wacce ta share shekaru hudu tana fama da tashin hankali.
‘Daya daga cikin matan da aka yiwa fyaden ta zargi Akechak da umartar sojojin dake karkashinsa su yiwa mata ma’aikatan agajin fyade a otel din Terrain dake Juba cikin watan Yulin shekarar 2016.
Facebook Forum