Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Kasar Kenya Ya Ce Dole Ne A Yi Zabe Ranar Alhamis


 Uhuru Kenyatta, shugaban Kenya
Uhuru Kenyatta, shugaban Kenya

Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta, yace dole ne a yi zaben shugaban kasar da aka shirya yi ranar Alhamis, ko da kuwa akwai ‘dan takarar jam’iyyar adawa Raila Odinga a zaben ko babu.

Zaben da aka shirya yi ranar Alhamis dai shine zaben shugaban ‘kasa na biyu a cikin wannan shekarar. Kotun kolin kasar Kenya ce ta yi watsi da sakamakon zaben farko da aka yi a ranar 8 ga watan Agusta, saboda zargin da tayi na cewa an tafka kura-kurai.

‘Dan takarar jam’iyyar adawa Raila Odinga ya janye kansa daga zaben da za ayi, yana mai cewa hukumar zaben Kenya ta gaza yin sauye-sauye don tabattarda adalci a zaben. Suma Hadakar jam’iyyun adawa sun nuna rashin amincewarsu ga hukumar zaben kan cewa bata shirya gudanar da zabe na gaskiya ba.

A jiya Litinin shugaba Kenyatta ya ce gwamnatinsa ta baiwa hukumar zaben dukkan kudin da take bukata da zata gudanar da aikin zaben.

A wata sanarwa da jakadan Amurka a Kenya ya fitar jiya Litinin amadadin kasashen yammacin duniya guda 20, ciki har da kungiyar tarayyar Turai, yace suna kira ga duk bangarorin da lamarin ya shafa a Kenya su hada kai don ayi zabe ingantacce.

Sai dai kuma ana zargin Ruth Odinga, kanwar ‘dan takarar jam’iyyar adawa, da laifin lalata kayayyakin hukumar zabe, da kuma karfafawa magoya bayansu su yi tashin hankali.

Shugaba Kenyatta ya kalubanci duk wani da zai yi kokarin barazana ko kaiwa masu zabe hari da cewa “kada su fasa.”

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG