Sake jaddadawa duniya cewa kungiyar Ecowas, na nan kan bakanta game da batun fitar da kudi na bai daya a shekarar 2020, shine makasudin taron da kungiyar tayi a birnin Yamai, wanda ya hada shugaba Muhammadu Buhari, na Najeriya da Alhassane Watara, Cote D’ Ivoire, da Nana Akufo Addo, na Ghana da Faure Gnassingbe na Togo, bugu da kara da shugaban rikon kungiyar Ecowas.
Shugaban kasar Nijar Muhammadou Issoufou, mai masaukin baki ya bayyana cewa an dade ana tafka ruwa kasa tana shanyewa saboda haka lokaci yayi da yakamata a gani a kasa domin cire dukkan wani shakku daga zujiyar talakawan yankin na Ecowas.
Samarda sassaucin hada hada cigaban kasuwanci da karfafa hanyoyin bunkasa tattalin arzikin kasashe goma sha biyar na yankin Ecowas, shine abinda ake fatar cimma a karkashin wannan tsari daya samo tushe a 1987.
Saboda haka shuwagabanin kasashe mambobi suka dage har sai hakarsu ta cimma ruwa inji Ministan harkokin Nijar, Ibrahim Yakuba.
Wannan shine karopn farko da ake shigar da Najeriya cikin jerin kasashen mambobin kwamiti mai alhakin tafiyarda aiyukan samarda kudaden bai daya duk kuwa da cewa kasar na rike da kashi saba’in daga cikin dari na baki daya na arzikin yankin Ecowas.
saboda haka shugaba Muhammadu Buhari yace Najeriya kasancewar wannan shine karon farko ta Najeriya ta kasance a cikin kwamitin nada wata uku kwamiti za suyi aiki a kuma yi taro a Ghana daga nan kuma za a san inda aka nufa.
Yanzu dai kasashen sun bayyana cewa zasu yi koyi da yadda kasashen Turai, suka shinfida tsarin kudaden Yuro, domin cika wannan buri batare da wata mishikila ba, za dai a gudanar da wani taron a watan Fabarerun 2018, a kasar Ghana, domin tsayarda tsarin wannan sabuwar tafiya.
Facebook Forum