Kwanaki biyu kafin a sake zaben shugaban kasar Kenya, an harbi direban mataimakiyar babban jojin kasar, Philomena Mwilu, inda aka raunata shi a jiya Talata, a cewar ‘yan sandan birnin Nairobi.
An harbi direban ne a kafada, wanda kafafen yada labaran cikin gida suka bayyana shi da sunan Titus Musyoka, wanda kuma wasu rahotanni suka bayyana shi a matsayin mai tsaron lafiya.
‘Yan sanda dai sun ce babu wani rahoto da ya fayyace ko ita mai shari’a Mwilu na cikin motar a lokacin harin.
Zaben da za a yi a gobe Alhamis, shi ne karo na biyu da al’umar kasar ta Kenya ke yunkurin yi na zaben shugaban kasa a bana.
Kotun kolin kasar ta yi watsi da sakamakon zaben farko da aka yi a ranar 8 ga watan Agusta, domin a cewarta, an tafka kurakurai.
A watan da ya gabata, babban mai shari’ar kasar ya ce ana yi wa alkalai barazana, tun bayan hukuncin da suka yanke gameda zaben farko.
Shugaban ‘yan adawa Raila Odinga, wanda ya janye takararsa daga wannan zaben, ya yi kira ga magoya bayansa da su yi zanga zangar nuna matsalolin da ke tattare da hukumar zaben kasar.
An samu barkewar tarzoma tsakanin ‘yan sanda da masu bore, yayin da hukumomi suka haramta yin zanga zanga a manyan biranen Kenya a makon da ya gabata.
Facebook Forum