Ana Cigaba Da Garkuwa Da Mutane a Adamawa Da Taraba

Wasu yaran da aka ceto kwanan baya

Kamar yadda al'amarin ya ke a wasu jahohin Najeriya, jahohin Adamawa da Taraba na fama da matsalar sace mutane don nemar kudin fansa.

Kamar yadda alkalumma ke nunawa ko a kasa da mako guda masu garkuwan sun yi tu'annuti da dama a jihohin Adamawa da Taraba inda suka sace wasu malaman jami'ar kimiyya da fasaha ta Modibbo Adama dake Yola, da wani dagaci a yankin Maiha da kuma a won gaba da suka yi da wasu mutum hudu a garin Munkin ciki harda Sarkin Fulanin Zing dake jihar Taraba.

To sai dai kuma, yayin da Jama'an jihohin biyu ke cikin zulumi da fargaba su kuwa hukumomin tsaro cewa suke suna nasu kokari, kamar yadda kakakin rundunan yan sandan jihar Adamawa SP Othman Abubakar yayi karin haske.

Su dai yan garkuwan kan bayyana kudaden da za'a basu kafin su sako wanda suka sace, yayin da a wasu lokutan yakan zo da karar kwana, batun da ake dangantawa da karancin jami'an tsaro.

Ga dai wakilinmu Ibrahim Abdul'aziz da cikakken rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

Wasu 'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Jama'a