Ana Ci Gaba Da Tafka Ruwa Kamar Da Bakin Kwarya A Jihar Texas

Yau talata ana ci gaba da keta ruwa kamar da bakin kwarya a kudu maso gabashin jihar Texas, yankin da ruwan sama mai karfin gaske ya haifar da ambaliya a daya daga cikin birni mafi girma na kasar Amurka.

Masu binciken yanayi sun kiyasta cewa ruwan zai ragu tsakanin ma’aunin centimita 25 zuwa 50 kafin ruwan ya dauke daga yankin a ranar Alhamis. Wannan na daga cikin karin ma’aunin centimita 90 na ruwan da aka riga aka tafka a wasu daga cikin yankunan wanda ya hada da birnin Houston.

Ambaliyar ruwan sama ta mamaye gigaje da hanyoyi inda ma’aikatan ceto ke ta ci gaba da faman taimakawa jama’a.

Magajin garin Houston Sylvester Tuner, ya ce daga ranar litini an kwashe sama da mutane dubu 3, wasu dubu 8 kuma suna matsuginai. Ya kuma bayyana cewa akwai rahotannin mutane uku da suka rasu sakamakon ambaliyar.

Gwamnan jihar Texas Greg Abbott, ya fadawa manema labarai cewa ya tura jami’an kai daukin gaggawa 1500, na daukacin jihar domin su taimaka.