An kakabawa kasar Venezuela takunkumin ne da nufin nuna cewa, “Amurka ba zata kyale haramtacciyar gwamnati ta dore a yankin, da zata kuntatawa al’ummarta ba,” bisa ga cewar mashawarci kan harkokin tsaro H.R. McMaster a hirarsu da manema labarai.
Shugaba Donald Trump ya rabbata hannu tare da zartar da takunkumin jiya jumma’a da ya haramta hulda da gwamnatin Maduro da kuma kamfanin man kasar PDVSA.
Sakataren ma’aikatar kudin Amurka Steve Mnuchin ya fada yayin hira da manema labarai a fadar White House cewa, takunkumin zai sa Maduro ya gaza yiwa mukarrabansa na siyasa da kuma masu goyon bayan gwamnatin toshiya.
Da yake maida martani, shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro ya yi allah wadai da takunkunin da yace takunkumin sun sabawa dokokin kasa da kasa, kuma an sanya sune da nufin ganin kasar ta gaza sauke nauyin da ya rataya a wuyanta.
Facebook Forum