Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Donald Trump Na Fuskantar Suka Daga 'Yan Jam'iyyarsa


Ana ci gaba da samun rashin goyon baya ga hukuncin da shugaban Amurka Donald Trump ya yanke na yiwa tsohon babban jami'in 'yan sandan jihar Arizona afuwa, bayan da aka same shi da laifin nuna wariya.

Kakakin majalisar Wakilan Amurka Paul Ryan ya bayyana cewa, bai goyi bayan shawarar da shugaba Donald Trump ya yanke ta yiwa tsohon babban jami’in ‘yan sandan jihar Arizona Joe Arpaio afuwa ba, kasa da wata guda bayan samunsa da laifin nuna wariya.

Mai Magana da yawun kakakin majalisar, Doug Andres ya fada a wata sanarwa cewa, “Jami’an kiyaye doka da oda, suna da hakki na musamman, na kare kowa a Amurka. Bai kamata mu kyale wani ya yi tsammanin, ahuwar na nuna cewa, yanzu an dage wannan nawayar ba.

Dukan ‘yan majalisar dattijai biyu dake wakiltar jihar Arizona, John McCain da Jeff Flake suma sun kushewa wannan yunkurin.

A sanarwar da fadar shugaban kasa ta fitar ranar jumm’a da yamma tace, Arpaio, “ya shafe dukan rayuwarsa yana kare al’umma daga miyagun laifuka da kuma shiga kasar ba tare da izini ba. Kuma yanzu Jami’in dan sanda Joe Arpaio mai shekaru tamanin da biyar a duniya, bayan shafe sama da shekaru hamsin yana yiwa kasa aiki, ya cancanci shugaban kasa ya yi masa ahuwa.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG