Anasa ran ganawar ta karshen mako zata shawo kan matsalar da taki ci taki cinyewa na gina katanga a kan iyakar Amurka da Mexico da shugaban na Amurka Donald Trump ke niyar yi.
Trump ya fada a jiya Juma’a cewa an yi tattanawa mai ma’ana a ganawar da ya yi da shugabannin majalisun tarayya a kan warware batun rufe gwamnati biyo bayan rashin fahimta da aka samu a kan dala biliyan biyar da dubu dari shida na gina katangar.
Amma shugabannin majalisun na bangaren Democrats sun fadi akasin haka a kan ganawa da suka yi da fadar White House.
Kakakin majalisar wakilai Nancy Pelosi ta Democrat, da aka rantsar da ita a shekaranjiya Alhamisa a shugabancin majalisar, ta kira ganawar ta sa’o’I biyu da mai cike da takaddama. Ta ci gaba da batun da nace akai cewa sai an bude gwamnati kana a warware batun kudin gina katangar.
Shima Chuck Schummer shugaba a majalisar dattawa ya fadawa manema labarai cewa, shugaban kasa ya yi barazanar rufe gwamnati tun da dadewa wurin watanni ko kuma shekaru.