Shekarar 2018 ta zo ta kuma wuce da al'amura da dama na farin ciki da kuma na bakin ciki; na alheri da kuma na bala'i. Sannan an tsoma kafa cikin shekarar 2019 wadda har yanzu ba a tabbatar da abin da za ta zo da shi ba. To amma ana iya kyautat zaton za ta zo da wasu abubuwan da ake ganin alamunsu tun daga yanzu.
Don haka na tuntubi mai sharhi kan al'amuran yau da kullum a Najeriya, Malam Amin Sule don ya ma na fashin baki da tsokaci kan abubuwan da su ka gabata a 2018 da kuma hasashen abubuwan da ake ganin wata kila su faru a 2019.
Malam Aminu ya ce cikin abubuwan da su ka girgiza shi a 2018 har da zubar da jini da aka yi ta yi a jahar Zamfara, inda wasu 'yan bindiga marasa imani su ka yi ta hallaka mutane ba ji ba gani. Ya ce zubar da jinin da aka yi ta yi a Najeriya abin takaici ne. A matakin kasa da kasa kuma, ya ce ya yi mamakin kashe dan jaridan Saudiyya dinnan mai suna Jamal Khashoggi da aka yi a karamin ofishin jadadancin Saudiyya da ke Istanbul na kasar Turkiyya.
Malam Aminu Sule ya kuma ce shirin Shugaban Amurka Donald Trump na janye sojojin Amurka a Siriya ka iya zama alheri a 2019 idan aka tsara shi da kyau. Ya kuma yaba da shawarar da bangaren al-Barnawi na Boko Haram ya yanke na sassautawa a gwagwarmayarsu.
Ga dai cikakken hirar: