Ana Ci Gaba Da Dambarwa A Kan Zaben Shugaban Kasar Laberiya

Ana ci gaba dambarwar zaben shugaban kasa a Laberiya inda da kotun kolin kasar ta dage zaben fidda gwanin da aka shirya yi kwanan nan har sai Illamasha'Allah, ‘yan sa’o’i kafin a bude rumfunan zabe.

Bayannan da ke bullowa daga baya-baya sun nuna cewa, dan takara George Weah, na kasar Laberiya, ya musanta cewa yana so tsohon shugaban kasar, Charles Taylor wanda aka same shi da laifukkan yaki, ya koma kasar.

Weah, ya fadawa Muryar Amurka, cewa rahotannin dake nuna cewa yana kokarin ganin tsohon shugaba Taylor, ya dawo farfaganda ce kawai, kuma zance ne mara tushe.

Tsohon mai binciken majalisar dinkin duniya Alan White, ya fadawa Muryar Amurka kwanan nan cewa, Weah yana so ya maido da Taylor, Laberiya inda an zabe shi.

Abokiyar takarar Weah, ita ce Tsohuwar matar Taylor, Jewel Howard Taylor. Mr. White ya ce Jewwl Howard ta yi magana a fili akan hana dawo da manufofin tsohon maigidanta.

Tsohon shugaba Taylor na zaman gidan kaso yanzu haka har na tsawon shekaru 50 a Burtaniyya, bayan da wata kotu ta musamman a Saliyo, mai samun goyon bayan majalisar dinkin duniya ta same shi da aikata laifukan keta hakkin bil’adama.