Babban abin damuwa shine wannan rikicin yana kara zafi ne a wannan lokaci da ya rage wata guda a gudanar da gasar kokawa ta shekara shekara a cikin kasar abin da al’ummar kasar ke ganin rashin yin gasar zai yi mummunar tasiri ga wasan kokawa a Nijer.
Wasu yan kasar ta Nijer suna zargin cewar matakin da hukumomi suka dauka na rushe kungiyar wasan kokawa akwai lauje cikin nadi. Wasu yan kasar sun ce wasan kokawa yana hada kan al’ummar Nijer don haka yakamata a warware wannan matsalar.
Kasim Muktar shine ministan wasanni motsa jiki a jamhuriyar Nijer kuma yace wadanda gwamnati ta basu amanar rikon wannan kungiyar kokawa basu yi aikinsu da kyau ba. Ministan yace rikice rikice a hukumar kokawar ya haifar da rashin ci gaba wannan wasan.
Facebook Forum