Wata sanarwa da ta fito daga ofishin shugaban kasar Tanzania John Magufuli, ta ce yanke shawarar da kotun ta yi zai kawo cikas ga kokarin kawo sulhu da kwamitin kasasehn gabashin Afirka, kwamitin da aka ‘dora masa nauyin warware rikicin Burundi.
Shi dai wannan kwamiti yana karkashin jagorancin shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni da kuma tsohon shugaban kasar Tanzania Benjamin Mkapa.
Jiya Asabar Museveni ya zargi kutun ICC da yin katsalandan ga aikin kwamitin kungiyar kasashen gabashin Afirka, wanda yake shugabanta, kasashen yankin dai sun hada da Tanzania da Uganda da Kenya da Rwanda da Burundi da kuma Sudan ta Kudu.
Tun ranar Juma’a dai gwamnatin Burundi ta ce ba zata baiwa kotin ICC hadin kai a wannan bincike ba. A kwanan nan ne dai kasar dake a gabashin Afirka ta yanke hukuncin janyewa daga kutun, amma kutun tayi jayayyar cewa janyewa daga kotun ba zai hana kotun bincikar laifin da aka aikata kafin janyewar.
Facebook Forum