Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Sudan Ta Kudu Ta Karyata Cewa An Saki Babban Hafsan Sojan Kasar


Shugabanni daga kasashen Afirka da duniya sun kasance wurin bukukuwan a Nairobi domin tunawa da ranar -- Ali Bongo Ondimba, Ghana; Goodluck Jonathan, Nigeria da Salva Kiir, South Sudan.
Shugabanni daga kasashen Afirka da duniya sun kasance wurin bukukuwan a Nairobi domin tunawa da ranar -- Ali Bongo Ondimba, Ghana; Goodluck Jonathan, Nigeria da Salva Kiir, South Sudan.

Gwamnatin kasar Sudan Ta Kudu ta karyata cewa ba a saki babban hafsan sojan kasar ba da akewa daurin talala.

Gwamnatin kasar Sudan ta Kudu ta karyata cewa sam ba gaskiyta bane cewa an saki tsohon babban hafsan sojan kasar Janar Paul Malong bayan an yi masa daurin talala nas tsawon watanni 6.

Ministan yada labarai na kasar Michael Makuei ya shaidawa wannan gidan Radiyon cewa, zuki ta mallaki ne labarain da kafofin yada labaran da suka ruwaito wannan wannan labarin, yace babban hafasan yana na tsare a cikin gidan sa.

Sai dai a wuri daya matar ta Malong shaidawa Muryar Amurka tace an saki mijin nata ne ranar Alhamis akan dalilin rashin lafiya.

Amma kuma sai kwaran jiya matar ta janye wannan kalamai nata tana cewa mijin nata dai ya kusa kamala shirin ganin an sake shi.

A tattaunawar da akayi da ita ta wayar tarho daga kasar Kenya inda take tace yanzu haka yana Juba.

A cikin watan Mayu ne dai shugaba Kiir ya dauki wannan mataki akan babban hafsan sojankasar biyo bayan murabus din da wasu manyan hafsoshin kasar suka yi murabus tare da zargi shi janar Malong da nuna kabilanci a cikin ayyukan sojojin kasar, kana ya bar sojojinkasar suna aikata laifuffukan yaki.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG