An Yi Taron Bita Na Hukumar Leken Asirin Tsaron Najeriya

  • Ibrahim Garba

Wasu manyan sojojin Najeriya.

An hori jami'an tsaron da za a tura ofisoshin jakadancin Najeriya da ke kasashen waje da su kasance masu kare kasarsu cikin ayyukansu.

Babban Hafsan Tsaron Najeriya Janar Abayomi Gabriel Olonishekin ya yi gargadi ga jami’an tsaron da za a tura ofisoshin jakadancin Najeriya a kasashen ketare, da su kasance masu aiki tukuru kuma cikn gaskiya da rikon amana don kare kasarsu da kuma taimaka ma gwamnatin Najeriya a kokarinta na kawo sauye-sauyen cigaba.

Babban Hafsan Tsaron ya yi wannan jawabin ne a wurin taron bitar. Tunda farko, Shugaban Hukumar Leken Asirin Tsaron Najeriya Air Vice Marshal Monday Morgan ya ce hukumar za ta cigaba da kara kaimi wajen kare Najeriya daga duk wata barazana.

Wani tsaohon Hafsan sojin sama da ya kware a harkar tsaro ya ce jami’an tsaron da za a tura kasashen wajen za su rika turo ma Najeriya bayanai ne na sirrin tsaron kasa, kamar yadda tsarin diflomasiyya ya amince da shi.

Ga wakilinmu Hasaan Maina Kaina da cikakken rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

An Yi Taron Bita Na Hukumar Leken Asirin Tsaron Najeriya- 1'55''