An yi ruwan bama bamai a babban birnin kasar Libya

Gine ginen gwamnati da aka lalata a Tripoli babban birnin kasar Libya,

Kungiyar tsaro ta NATO ta yi ruwan bama bamai a abban birnin Libiya jiya Talata, a daidai lokacin da dakarun ‘yan tawaye ke ikirarin korar dakarun gwamnati nesa daga birnin bakin gaba na Misrata

Kungiyar tsaro ta NATO ta yi ruwan bama bamai a abban birnin Libiya jiya Talata, a daidai lokacin da dakarun ‘yan tawaye ke ikirarin korar dakarun gwamnati nesa daga birnin bakin gaba na Misrata, da a ka yi wa kawanya. NATO ta ce an auna wata cibiyar bayar da umurnin soji ne na dakarun da ke biyayya ga gwamnati, a hare-haren jiragen saman da aka kai birnin Trabulus. Mazauna wurin sun ce daya daga cikin bama baman ya fada kan wani ginin cibiyar sojojin Libiya da ake ajiye bayanan sirri. Jami’an NATO sun sake karyata zargin cewa suna auna shugaban Libiya Moammar Gaddafi ne to amma wani bam da ya fada gidan na Mr. Gaddafi ya sa hayaki mai yawa ya yi sama. A Mistara, wani mai magana da yawun dakarun ‘yan tawayen yace mayakan ‘yan tawayen sun dada tura dakarun gwamnati can baya da misalin nisan kilomita 15 daga birnin a kokarin dakarun ‘yan tawayen na dannawa ga garin Dafniya. Kanar Ahmed Bani ya kuma ce ‘yan tawayen sun kakkabe dakarun da ke biyayya ga Gaddafi daga kewayen filin jirgin saman bayan kazamin fadan da aka yi na kwanaki biyu. A gabashin Libiya kuma, ‘yan tawaye sun ce sun kara nausawa zuwa Ajdabiyya da Brega.