Kungiyar NATO ta ce ta kai hare-hare ta sama jiya asabar a birnin Tripolin Libya, amma ba zata iya gaskata rahotannin cewa harin da ta kai ya kashe dan shugaba Muammar Gaddafi da kuma wasu jikokinsa uku ba.
Leftana-janar Charles Bouchard na NATO yace sojojin taron dangi sun kai hari kan wani ginin hedkwatar ayyukan soja a unguwar Bab al-Azizya ta Tripoli, amma kuma ya kara da cewa sojojinsa ba su ware wani mutum domin kai masa hari ba. Yace NATO tana takaicin duk hasarar rayuka, musamman ma na fararen hular da ba su san fari ba balle baki.
Tun da fari a jiya asabar, kakakin gwamnatin Libya, Moussa Ibrahim, yace NATO ta kai hari a kan gidan dan autan Gaddafi, Saif al-Arab Gaddafi mai shekaru 29 da haihuwa, ta kashe shi tare da wasu jikokin shugaba Gaddafi su uku.
Kakakin na gwamnatin Libya yace shugaba Gaddafi da matarsa su na gidan a lokacin da aka kai wannan harin, amma babu abinda ya same su. Amma yace mutane da dama a cikin gidan sun ji rauni.
An nunawa ‘yan jarida wannan gida, inda suka gane ma idanunsu barna mai yawa da ta wakana.
Moussa ya bayyana wannan lamari a zaman yunkurin kai tsaye na neman kashe shugaba Gaddafi.
A lokacin da wannan labari ya bazu, mutane a cibiyar ‘yan tawaye dake birnin bengazhio sun fito waje su na harba bindigogi a sama tare da yawo cikin mota su na matsa hon domin bayyana murnarsu.
Tun da fari a jiyan, NATO ta ki yarda da tayin Gaddafi na tattaunawa domin kawo karshen wannan rikici a Libya.