Ana cigaba da jimami da alhini bayan da aka binne gawar marigayi babban hafsan mayakan kasan Najeriya a Abuja Laftanar Janar Taoreed Lagbaja.
An binne shi ne a makabartar kasa dake babban birnin tarayyar Najeriya abinda ya kawo karshen kwanaki 2 da aka shafe ana gudanar da bukukuwan jana’izar da aka soma tun daga Legas a farkon makon da muke ciki.
An binne gawar ne da misalin karfe 4.41 na yammaci bayan wani biki da aka shafe fiye da sa’o’i 2 ana gudanarwa.
Akwatin gawar nade da tutar Najeriya, ya isa makabartar ne da misalin karfe 3 na yamma a cikin wata farar motar daukar gawa bayan gudanar da addu’o’i a babbar cibiyar mabiya addinin Kirista dake Abuja.
Gabanin binne gawar, an gudanar da taron addu’o’i a filin faretin dake shelkwatar rundunar sojin Najeriya, dake barikin Mogadishu, a Abuja a jiya Alhamis.