WASHINGTON DC - Gobarar ta shafi wasu gine-gine guda 3 ne, ciki harda wasu benaye masu hawa bibiyu da wani bene mai hawa daya, a bangaren kasuwar daya fi shahara da kasuwancin tufafi da takalma da jakunkuna.
Tuni dai jami'an hukumar kwana-kwana da bada agajin gaggawa ta jihar Legas da sauran hukumomin bada agaji suka isa wurin da al'amarin ya faru inda suka kaddamar da aikin kashe gobarar.
A cewar Shugabar Hukumar Kwana-Kwana ta jihar Legas, Margaret Adeseye, cibiyoyin kashe gobara na unguwannin Ebute Elefun da Ilupeju da Alausa sun tura jami'ai da kayan aiki domin taimakawa wajen shawo kan gobarar wacce tuni aka kaddamar da yaki da ita.
Har yanzu dai ba'a kai ga gano musabbabin tashin gobarar ba, amma an kaddamar da bincike akan hakan. Haka kuma, ba'a kai ga tantance asarar rai ko jikkata ba
Adeseye ta bukaci mazauna yankin su baiwa jami'an bada agajin gaggawa hadin kai tare da kaucewa wurin domin kiyaye lafiyarsu.