Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Kwastan Ta Kama Muggan Kwayoyi Da Makamai A Tashan Jiragen Ruwa ta Legas


Kwanturolan kwastan, Dera Nnadi, yana nuna makaman da aka kama a tashan jiragen ruwan Legas.
Kwanturolan kwastan, Dera Nnadi, yana nuna makaman da aka kama a tashan jiragen ruwan Legas.

Hukumar Kwastan reshen tashan jiragen ruwa ta Tin Can ta kama wasu tarin makamai da kayan soji da alburusai da kuma muggan kwayoyi da aka yi yunkurin shigowa dasu Najeriya ta hanyan sumogal.

LEGAS, NAJERIYA - A wata sanarwa da hukumar ta kwastan ta fitar a juma'ar nan na cewa daga cikin muggan kwayoyin da aka kama sun hada da nauyin colorado da hodar iblis da kuma hodar koken.

A cewar kwanturolan kwastan mai kula da tashan jiragen ruwa ta Tin Can, Mr Dere Nnadi wasu jami'an hukumar ne suka gano inda aka boye kwayoyin da makamai a wasu sundukai na kaya da akayi yunkurin shigo dasu Najeriya.

Makaman da aka kama sun hada da bindigogi kirar rifle masu sarrafa kansu da kansu.

Kuma yanzu haka dai hukumar ta kwastan tace tana tsare da wasu mutane dake da alaka da haramtattun kayan da aka kama.

Najeriya ta dade tana fama da rashin tsaro wanda ya haifar da mutuwar mutane da dama a fiye da shekaru 10. Sauda yawa dai shugabanni da masu kula da harkokin tsaro na zargin ana shigowa da akasarin makaman ne daga kasashen ketarare, abunda kuma keci gaba da ruruta wutar rikicin.

Mako guda daya wuce kenan da yan bindiga suka sace yaran makaranta kusan 300 a kauyen kuriga dake jihar kaduna.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG