Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Zanga-Zanga A Legas Duk Da Gargadin Yan Sanda


Masu Zanga-zangar Tsadar Rayuwa a Legas
Masu Zanga-zangar Tsadar Rayuwa a Legas

Matsin tattalin arziki a fadin Najeriya ya harzuka ‘yan kasa inda suka bazama kan tituna a wasu jihohi don nuna rashin jin dadinsu dangane da tashin gwauron zabin kayayyakin abinci da tsadar rayuwa a kasar.

Birnin Legas na daya cikin biranen da mutane suka fantsama kan tituna domin zanga-zanga, duk da gargadin da kwamishinan ‘yan sandan jihar Lagas, Adegoke Fayoade, ya yi a ranar Lahadi, amma ya musanta zargin kamar yadda kakakin rundunar 'yan sandan jihar Legas ya wallafa a shafinsa na X.

SP Benjamin Hundeyin ya ce "Tabbas wannan ba gaskiya bane. Rundunar ‘yan sandan ta isa wurin da lamarin ya faru domin tabbatar da tsaron da ya dace ga kungiyar farar hula (CSOs) da kuma hana bata-gari su yi awon gaba da zangar-zangar.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Legas, CP Adegoke Fayoade, ya yi wa masu zanga-zangar jawabi kafin su fara. Ya zuwa yanzu dai an gudanar da zanga-zangar cikin lumana ba tare da wata matsala ba.

Jawabin Kwamishinan Yan Sandan Legas Na Kare Masu Zanga-zanga
Jawabin Kwamishinan Yan Sandan Legas Na Kare Masu Zanga-zanga

Wasu hotunan bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta, sun nuna masu zanga-zanga a karkashin wata kungiyar kare hakkin bil'adama mai suna "Take It Back Movement" dauke da kwalaye da rubutu daban-daban a yankin Ojuelegba da ke jihar Legas.

An gudanar da irin wannan zanga-zangar a jihohin Edo da Osun, inda masu zanga-zangar suka yi maci kan tituna dauke da rubuce-rubuce daban-daban kamar su “End Economic Hardship” da “FG End the Hunger in Nigeria Now,” duk don nuna bacin ransu.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG