Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tinubu Ya Kaddamar Da Layin Dogo Na Zamani A Legas


Layin Dogo
Layin Dogo

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya kaddamar da layin dogo 'Red line' na zamani a birnin Legas.

Aikin mai tsawon kilomita 37 zai karade wasu manyan yankunan birnin, wanda shi ne cibiyar kasuwancin kasar.

A kullum za’a dinga jigilar akalla fasinjoji kusan dubu dari biyar (500,000), a tsakanin Agege da Oshodi da Ikeja da Mushin da Yaba zuwa Oyingbo.

Da yake jawabi yayin kaddamar da tsarin sifurin na Red line, shugaba Tinubu ya sake jaddada kudurin gwamnatinsa na inganta abubuwan more rayuwa a kasar.

Tinubu ya yi hasashen cewa, layin dogo zai kawo babbar dama ga tattalin arzikin jihar, yana mai nuna godiya ga hukumar LAMATA da abokan huldar da suka tabbatar da kammala kashi na farko na aikin.

Shugaban kasar ya ce babu gudu, ba ja da baya dangane da sauye-sauyen da gwamnatinsa ta kudiri aniyar aiwatarwa.

Idan ba’a manta ba watan Satumbar shekarar 2023 ne tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da layin dogo na 'Blue line' a jihar wanda ya tashi daga Marina zuwa unguwannin Alaba da Mile 2 da Festac da Alajika da jami'ar LASU ya dangana zuwa Maintenance Deport.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG