Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Za Ta Kaddamar Da Kofofi Masu Amfani Da Na’ura A Tashoshin Jiragen Saman Kasar A Watan Maris


Filin Jirgin Saman Mallam Aminu Kano 1
Filin Jirgin Saman Mallam Aminu Kano 1

A kokarinta na saukakawa matafiya zirga-zirga a filayen tashi da saukar jiragen kasar, gwamnatin tarayya ta sanar da shirinta na kaddamar da kofofi masu amfani da na’urar lantarki a filin saukar jiragen saman kasa da kasa a Najeriya a watan Maris me kamawa.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, wanda ya bayyana hakan a Abuja jim kadan bayan kammala rangadin duba kayayyakin aiki a tashar jiragen saman, yace yanzu za’a samu sauki wajen daukar hoton takardun tafiye-tafiye idan aka kaddamar da kafofin masu amfani da na’ura a filayen saukar jiragen saman.

Ministan ya kuma gudanar da rangadi a cibiyar da ayyukan hukumar kula da shige da ficen Najeriya sa’annan ya baiwa ‘yan Najeriya tabbacin cewar kammala ginin cibiyar zai inganta yanayin tsaro a Najeriya.

A cewar Tunji-Ojo, samun yawaitar kofofin masu amfani da na’ura, zai saukaka zirga-zirgar fasinjoji a tashoshin jiragen saman kasar.

Ya kara da cewar, “na yaba da irin ingancin aikin da aka yi. Ina farin cikin cewar ‘yan Najeriya zasu samu sauki.”

“Da zarar an kammala wannan aiki, ‘yan Najeriya ba zasu sake neman agajin jami’an shige da fice ba inda suka shigo kasar nan. Abinda kawai ake bukata shine mutum ya sanya fasfo dinsa na’ura ta dauki hotonsa, ta bude masa kofa, nan take bayanansa zasu fito yayi tafiyarsa, mutum baya bukatar haduwa da wani jami’in shige da fice indai ba me laifi ba ne.”

Ministan ya ci gaba da cewar hakan zai inganta tsaron kasar.

Yace jihar Legas zata samu kofofin na’urar guda 17 a yayin da Abuja za ta samu 10 sai kuma filayen saukar jiragen saman Fatakwal da Kano da zasu samu biyar-biyar kowannensu sai kuma Enugu me kofa hudu.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG