A yau Juma’a, alkalin birnin New York din da ya jagoranci shari’ar ba da toshiyar bakin da ake yiwa Donald Trump ya yankewa zababben shugaban kasar hukuncin “sallama ba tare da gindaya wani sharadi ba,”
Abin da ke nufin cewa ba zai fuskanci zaman gidan yari, tara, ko kuma gwajin halayya ba
“Wannan al’amari ne mai matukar takaici,” a cewar Trump da ke cikin bacin rai, inda yake magana ta na’ura daga gidansa na Florida sa’ilin da aka bashi damar yin jawabi ga alkalin.
“An yi haka ne da nufin bata mini suna domin in fadi a zabe,” a cewarsa.” Bani da laifi ko kadan. Ban aikata wani ba daidai ba,” a cewarsa.
Hukuncin na zuwa kwanaki 10 gabanin a rantsar da Trump a matsayin shugaban Amurka na 47.
“Kotun nan bata taba fuskantar irin wannan lamari da jerin al’amura masu daukar hankali ba,” kamar yadda alkali Juan Merchan ya bayyana gabanin ya yanke hukuncin. Hakika wannan shari’a ce ta musamman.”
Lauyoyin Trump sun yi ta yunkurin su dakatar da ci gaba da sauraron karar, wacce Merchan ya tsara a makon da ya gabata.