Bannon ya kai kanshi gidan yarin Tarayya da ke Danbury, Connecticut, inda ya shaida wa manema labarai da magoya bayansa da suka hada da 'yar Majalisar wakilan Amurka Marjorie Taylor Greene, cewa shi "fursunan siyasa ne" kuma "yana alfahari da zuwa gidan yari."
Ya dorawa ‘yan jam’iyyar Democrat da kuma babban mai shigar da kara na Amurka Merrick Garland alhakin hukuncin daurin watanni hudu a gidan yari da aka yanke masa.
Wasu gungun masu zanga-zangar ma sun isa wurin, suna ta kururuwa suna cewa, "maci amana!"
Bannon ya yi tsokaci kan abubuwan da suka faru a baya-bayan nan da suka hada da zaben Faransa wanda ya kai jam'iyya mai ra'ayin mazan jiya, dab da kafa gwamnati fiye da kowane lokaci, da kuma hukuncin da kotun kolin Amurka ta yanke wanda ya mayar da shari'ar kariya ta Donald Trump zuwa wata karamar kotu a Washington.
Bannon ya bayyana cewa, "MAGA na kara karfi, dubi abin da ya faru a Faransa jiya. Mutanen Faransa sun fara kwace kasarsu daga hannun masu ra’ayin maida kasar ta kowa. Sannan a safiyar yau Kotun Koli ta yanke hukunci da gagarumin rinjaye 6-3, babban abu ne. Ana yanke shawara a ko'ina, kuma za mu ci nasara. an kafa tarihi a cikin 90 da suka shige a duniya baki daya ."
An samu Bannon da laifuka biyu na raina Majalisa a 2022.
Wani alkali ya amince Bannon ya ci gaba da rayuwarsa ta yau da kullum cikin ‘yanci na kusan shekaru biyu yayin da yake daukaka kara a shari’ar, amma an umarce shi da ya fara hukuncin daurinsa bayan da wasu alkalai uku na kotun daukaka kara na D.C suka amince da hukuncin da aka yanke masa a watan Mayu.
Kotun kolin kasar ta yi watsi da wata kara da Bannon ya shigar a ranar Juma’a, ta hana shi damar sake dage yanke hukuncin.
Ana sa ran Bannon zai shigar da kara a daukacin kotunan daukaka kara na D.C.
Dandalin Mu Tattauna