An Yanke Kafar Shahararren Jarumin Fina-Finan Nollywood Mr Ibu

Mr Ibu

Jazimine Okafor, diyar fitaccen jarumin fina-finan Nollywood John Okafor, wanda aka fi sani da Mr. Ibu ce ta tabbatar da cewa an yanke kafar mahaifinta.

Likitoci sun yanke kafar shahararren jarumin fina-finan Nollywood na Najeriya, John Okafor, a wani yunkuri na ceto rayuwarsa.

Tun a watan Oktoba ne Mr Ibu da iyalansa suka nemi taimakon al'umma kan irin halin da ya ke ciki na rashin lafiya, wanda a karshe ya yi sanadiyar rasa kafar sa.

Okafor, wanda ya yi fice a fina-finai dabam-dabam, ya yi suna ne tun bayan da ya fito a wani fim mai suna 'Mr Ibu in London, asalin lakanin Mr Ibu kenan.

A cikin wata sanarwa, iyalan shahararren jarumin sun bayyana cewa likitoci sun yanke daya daga cikin kafafuwan jarumin domin ceto ransa.

Labarai a watan Oktoba sun bayyana yadda jarumin ya kamu da cuta, inda har ta kai shi ga neman taimakon kudin da za'a yi masa jinya.

A karshe iyalan jarumin sun yi godiya ga daukacin mutanen da suka taimaka musu, tare da fatan jarumin zai yi wa al'umma godiya da kansa da zarar ya samu saukin yin hakan.