Garin Birni N'Konni, shine babban gari a Jamhuriyar Nijar mafi kusa da wata kasa ta ECOWAS, kasancewa mita 500 ne kacal tsakanin Jami'an tsaron Nijar da takwarorin su na Najeriya a wannan iyakar ta Birni N'Konni a jahar Tahoua da karamar hukumar Illela ta tarrayar Najeriya.
Tun lokacin da taron shugabanin kasashen kungiyar ta ECOWAS na karshe a makon jiya da ya wakana a Abuja, shugabanin suka yanke shawarar kakabawa Jamhuriyar Nijar takunkumai tare da bai wa askarawan kasa da suka karbe mulki daga Mohamed Bazoum sati guda na mayar da shi kan kujerar sa, ra'ayoyi suka soma cin karo da juna game da tasiri ko akasin haka na kulle iyakokin kasashen ECOWAS da Nijar.
Wadansu yan Najeriya da ke kasuwancin kai komo a kan iyakar, sun ce, takunkumai na hana shiga da fita a Nijar, na iya shafuwar tattalin arzikin kasashen 2 da al'ummomin su.
Sai dai a cewar wani manazarcin al'amuran yau da kullum, barazanar takunkumin tauna tsakuwa ne kawai don aya ta ji tsoro, domin ba zai yi wani tasiri ba.
Yan kasuwar na Nijar da ke shiga Najeriya suna kawo abinci a Nijar, cewa suka yi takunkumi na iya jefa mutanen Nijar da ma na Najeriya da ke wannan yankin a cikin wata matsala.
Malam Maman Hassan masani tattalin arziki ne, ya kuma ce akwai matsalolin da ke iya bijirowa da zaran an saka wa Nijar takunkumi kamar yadda ECOWAS ta yi barazana.
Yanzu haka iyakokin na Nijer na kulle, yayin da jama'a suka zura idanu don ganin menene zai faru bayan wannan barazanar ta ECOWAS da hadakar kasashen yammacin nahiyar Africa.
Saurari rahoton a sauti:
Your browser doesn’t support HTML5