Shugabannin ECOWAS sun gudanar da wani taron gaggawa kan juyin mulkin Nijar a birnin Abuja, inda suka yi Allah wadai da juyin mulkin tare da ci gaba da amincewa da zababbiyar gwamnatin shugaba Mohamed Bazoum kamar yadda kungiyar tarayyar Afirka AU da sauran kasashen duniya ke yi.
Kungiyar ECOWAS ta bukaci da a maido da tsarin mulkin jamhuriyar Nijar gaba daya, tare da daukar matakin tsare shugaban kasar Mohamed Bazoum, a matsayin wani lamari na garkuwa.
Idan har ba a iya cika bukatun ECOWAS cikin mako guda ba, shugabannin sun ce za su dauki dukkan matakan da suka dace don maido da tsarin mulkin Jamhuriyar Nijar.
Matakan takunkumin da ECOWAS ta kakabawa jamhuriyar Nijar sun hada da:
1. Rufe dukkan iyayokin na sama da kasa tsakanin kasashen ECOWAS da Nijar.
2. Tabbatar da hana zirga-zirgar jiragen sama na kasuwanci tashi ko zuwa Nijar.
3. Katse duk wata alakar kasuwanci tsakanin kasashen ECOWAS da Nijar.
4. Dakatar da dukkan wata hulda aiki, ciki har da ta makamashi.
5. Dakatar kaddarorin Nijar a bankunan kasuwanci.
6. Dakatar da Nijar daga samun dukkan tallafi da duk wata mu’amula da cibiyoyin kasuwanci.
7. Kakaba takunkumin hana tafiye-tafiye ga jami’an sojojin da ke da hannu da iyalansu, ciki har da dukkan wani da ya karbi mukami a gwamnatin ta soji.
Dandalin Mu Tattauna